1 1 Littafin tarihin asalin Yesu Almasihu, ɗan Dawuda wanda shi ma ɗan Ibrahim ne. 2 Ibrahim ya haifi Ishaku, Ishaku ya haifi Yakub, Yakub ya haifi Yahuda da ˈyanˈuwansa. 3 Yahuda ya haifi Ferez da Zera. Mamarsu kuwa Tamar. Ferez ya haifi Hezron, Hezron ya haifi Aram, 4 Aram ya haifi Amminadab, Amminadab ya haifi Nashon, Nashon ya haifi Salmon. 5 Salmon ya haifi Bowaz. Mamarsa kuwa Rahab ce. Bowaz ya haifi Obed. Mamarsa kuwa Rut ce. Obed ya haifi Yesse, 6 Yesse ya haifi Sarki Dawuda. Dawuda ya haifi Solomon. Mamarsa kuwa Batsheba wadda dā matar Uriya ce. 7 Solomon ya haifi Rehobowam, Rehobowam ya haifi Abiya, Abiya ya haifi Asa, 8 Asa ya haifi Yehoshafat, Yehoshafat ya haifi Yoram, Yoram ya haifi Uzziya, 9 Uzziya ya haifi Yotam, Yotam ya haifi Ahaz, Ahaz ya haifi Hezekiya, 10 Hezekiya ya haifi Manasse, Manasse ya haifi Amon, Amon ya haifi Yosiya, 11 Yosiya ya haifi Yekoniya da ˈyanˈuwansa, a lokacin da aka kwashi mutanen Yahuda zuwa bauta a ƙasar Babila. 12 Bayan da aka kai su Babila, Yekoniya ya haifi Sheyaltiyel, Sheyaltiyel ya haifi Zerubbabel, 13 Zerubbabel ya haifi Abihud, Abihud ya haifi Eliyakim, Eliyakim ya haifi Azor, 14 Azor ya haifi Zadok, Zadok ya haifi Akim, Akim ya haifi Eliyud, 15 Eliyud ya haifi Eleyazar, Eleyazar ya haifi Mattan, Mattan ya haifi Yakub, 16 Yakub ya haifi Yusuf mijin Maryamu, Maryamu ta haifi Yesu wanda ake ce da shi Almasihu. 17 Wato dukan tsara daga Ibrahim zuwa Dawuda, tsara goma sha huɗu ce. Daga Dawuda zuwa lokacin da aka kwashi Israˈilawa zuwa bauta a Babila, tsara goma sha huɗu ce, daga bauta a Babila kuma zuwa haifuwar Almasihu, tsara goma sha huɗu ce. 18 Ga yadda aka haifi Yesu Almasihu. Lokacin da Yusuf yake neman Maryamu mamar Yesu da aure, tun ba a ɗaura musu aure ba, sai ya zama tana da ciki daga Ruhu Mai Tsarki. 19 Saurayinta Yusuf yana da kirki, kuma ba ya so yă ba ta kunya a cikin mutane, sai ya yi tunani yă sake ta shiru a ɓoye. 20 Amma yana cikin wannan tunani sai ga wani malaˈikan Ubangiji ya bayyana gare shi a mafarki, ya ce masa, “Yusuf ɗan Dawuda, kada ka ji tsoron ɗaukar Maryamu ta zama matarka domin cikin nan nata daga Ruhu Mai Tsarki ne. 21 Za ta haifi ɗa, za ka sa masa suna Yesu domin shi ne zai ceci mutanensa daga zunubansu.” 22 Dukan wannan ya faru ne domin a cika abin da Ubangiji ya faɗa ta bakin annabi cewa, 23 “Budurwa za ta yi ciki, ta haifi ɗa za a kuma sa masa suna Immanuwel.” Maˈanar Immanuwel ita ce, “Allah yana tare da mu.” 24 Da Yusuf ya farka daga barci, sai ya bi umarnin malaˈikan Ubangiji. Yusuf kuwa ya ɗauki Maryamu ta zama matarsa. 25 Amma bai san ta ba, sai bayan da ta haifi ɗanta, ya kuma sa masa suna Yesu.
Prev
Play
Next
Volume
Speed
0.7511.251.52